Wednesday, May 28, 2008

MAJALISAR DOKOKI TA AMURKA TAYI DOKA DAKE LAMUNCE MA KASAR ISRA’ILA YIN SAMA WAJEN KARFIN SOJA

Majalisar dokoki ta Kasar Amurka (wato congress) ta amince da dokan da take neman gaggauta kulla cinikin makamai da Kasar Isra’ila da Amurka, da bada Karin gudun mawan soja da Amurka takeyi wanda ze kai kimanin dala miliyan dari da hamsin na shekara ta 2009, kamar yadda dokan ta shardanta cewa dukkan wani makami da Amurka zata saida ma wata daga cikin kasashen larabawa kada yazami makami ne da ze iya kawo barazana ga zaman lafiyan kasar Isra’ila. Wannan ke nuna cewa Amurka tana da hannu cikin duk irin kisan gilla da Isra’ila takeyiwa Falasdinawa a kowace rana.

Sunday, March 9, 2008

ABIN KUNYA DA KO DABBA TAKE KYAMATA

Wani abin mamaki ne naci karo dashi wanda hankali baze taba tunanin yiwuwan aukuwan hakan ba, sannan koyaya mutum yakai da rashin kishi da lalacewa ze la'ance wannan danyen aikin, bugu da kari hakan yasa wasu yan iska marasa kima da sanin mutuncin addini suke batanci ga Manzan Allah Sallallahu Alaihi wasallam, da cewa wai shi ya karantar da aikata wannann mummunana aikin , wani dabban kuma daga kudu hakan tasa yake zagi ga al'adunmu da sarakunanmu cewa irin abubuwan da suke aikatawa kenan aboye kai abinda yafi muni ma shine ta'alikin da wani musulmi me suna Alhaji yayi na nadamam kasancewarsa musulmi saboda karanta wannan labarin. Allah ya kiyaye! To koma me zasu fada nidai yayin da na karanta wannan labari hankali na ya tashi da yin tunanin shin yanzu akwai wani mahalukin daze aikata hakan kuma musulmi a garin musulmi kai a garin da akema aiwatar da Shariar musulunci? to wane irin danyen aikine kuwa ya haifar da abubuwan da muka ambata? Shine Labarin Auwalu Muhammad mazaunin Unguwar Yakasai a cikin birnin Kano wannan aka gabatar dashi a gaban kotu wanda me sharia Maryam Ahmad Sabo ta jagoranta, shi da yayansa biyu Hadiza Yar shekara sha hudu, da kanwanta Nana Aisha yar shekara sha biyu, wanda mahaifiyarsu tayi yaaji saboda Uban wato Auwalu yana kwana dasu bayan ta hanashi yaki dena aikata hakan, ita Hadiza Yanzu haka tana dauke da cikin wata tara, - Allah yakiyaye Yarka matarka Jikanka yarka ko danka- ta bayyana ma koyu cewa sun tafi wajen yan uwansu amma uban yadawo dasu yana ya maidasu kaman matansa, kuma Shedanin Uban ko a jikinsa yana fita harkar kasuwancinsa seda aka kaishi kara be ko damuba, Allah ya shiryamu dashi gaba daya Amin. Daga jaridar Weekly trust 08/03/2008 me rahoto jaafar jaafar kano. To mudai mun kasa kunne muna jira muji hukuncin kotu. Saboda munsan hukuncin wanda yayi lalata da muharramansa shine kisa a shariar musulunci. Allah ya shirya mu Amin

Friday, January 18, 2008

KUNTATAWA FALASDINAWA AMFANIN WANENE?

KUNTATAWA FALASDINAWA AMFANIN WANENE?

Wahal-halu da Kungiyar Hamas take fuskanta da Kunci da take ciki, tun sanda ta sami nasaran lashe zabe wanda ya rikitar da shugaba Mahmoud Abbas da Kungiyarsa ta Fatah inda ta kasa zama zab’I na farko ga Mutanen Falasdin duk da irin iko dashi me girma a cikin gida da kuma waje, kai da temako ma sananne daga wajen Yahudawa masu mamaya, hakan yasasu k’in koda temakekeniya da Hamas, saboda K’okarin karya ta bayan tasami daman kafa hukuma, se Kuntata daga wajen (tsohuwar Kungiya) wanda har yanzu bata gushe ba tana zaune cikin rud’u cewa itace jagora a al’amarin.

Daga cikin wadanda suka bada gudunmawa wajen yin batanci ga Hamas har da Sannannun tsofaffin nan da Ihunsu yafi aikinsu yawa a kafafen watsa labarai na gida da na waje, musamman bayan abinda yafaru na gyara a goma sha hudu ga watan Yuni a Shekaran data shud’e, da tsoratarwa gameda Hamas, da sunan wai a rayawarsu tayi juyin Mulki ga hukauma, da nufin kafa kasa ta musulunci, kuma shin wacece hukuman in ba Hamasa ba?

hakika Mutanen Falasdinu sun d’and’ani daci guda biyu Na: Matakin rashin girmama dan Adam da Hukumar Mahmoud Abbas takeyi masu, da kuma: takurasu akan su kaurace ma Kungiyar Hamas, da kuma jefa shakka gameda Manufofinta, kai dama Manufofin wadanda suke cikinta, Saboda hakane sukayi aiki wajen baza duk kan k’okarinsu wajen sanya Isra’ila ta mamaye zirin Gazza, da karya Kungiyar, domin su koma kan iko bayan binkito Asirin me yawa da suke boye a wajensu na abin Kunya da sukayi, wanda aka bayyanar da cewa sun kasance suna tafiya akansu domin cimma burikansu na ciwo. Kuma daga cikin abin takaici shine hukuman tabada umarnin rufe Kungiyoyin agaji guda dari da uku (103) wadanda suke aikin jink’ai a Zirin Gazza da gabar Yamma da kogin Jordan, ta tuhuman wai sun sabama tsari! To me yasa ba’a gano hakaba se bayan rushewan sashin tsaronsu? Gaskiya itace Hukuman Falasdinawa karkashin Jagorancin Mahmoud Abbas da Manya Manayan magunansu masu k’iba suna zartar da ajandoji ne na Kasar Amurka da Isra’ila a cikin yakinsu ga ayyukan alkhairi wanda hakan abune dayake bayyane wajen kowa.

Wannan bari d’aya kenan, a gefe daya kuma zamuga wadanda ake ambata sun kunyata kawunansu, da kiraye – kirayen dasukewa mutanensu cewa su sake lale gameda hukumarsu da aka dakatar wato Kungiyar Hamas, wannan ke nuna kwadayinsu na Nufin sayan mutane day’an kudi marasa yawa alhali kuwa Falasdinawa sunfi karfin a yaudaresu, Sannan me yasa suka lalata wutan lantarki wanda suna daga cikin kayan more rayuwa na asali? Me yasa suka hana wasu kayan hukuma aiki, misali takardar tafiya wato Passport da yin sheda akan takardu da sauransu wanda rayuwa bata yiwuwa face dasu kuma shin akwai maslaha a yin hakan?

Tabbas wannan Kungiya ta marasa kishi, Bawai tana munana ma Hamasa bane kawai, A’a Falasdinawa take munanawa masu hakuri, wadanda suka wayi gari a yau basu da wata k’ima a wajen K’ungiyar Fatah me mulki dake jagoranci a Gabar yamma da kogin Jordan, kuma Falasdinawa sunfi karfin a rabasu da dabi’unsu da Manufofinsu. Hakika wasu daga kafafan watsa labarai na duniya sunyi nuni da cewa Kumgiyar Hamas zata kara K’arfi, wannan shine dalilin dayasa hukumar, tak’i ta dena aiwatar da dokokin korar ma’aikata, da jami’an tsaro da sauransu saboda zalunci da kuma kasancewarsu yan K’ungiyar Hamas ne.

Gasunan a yau suna ingiza wawaye a zirin Gazza wajen tada fitina da haifar da matsaloli, amma Mutanen Falasdinu masu hakuri abinda yasamesu na kunci ya ishesu. Kuma Mummunan Makirci baya komawa se ga masu aikata shi.

Thursday, January 10, 2008

Gamji Dan K'warai

Gamji Dan Kwarai, Allah yayi masa Rahama Amin. A 15-01-2008 yake cika shekaru 42 da kwanta dama, kuma har yanzu yana nan a zukatan Y'an Nijeriya, ba'a manta dashi ba, Anamasa Addu'a, Allah yajikan mazan K'warai. To wai Meyasa wanda suke raye ba'a ambatansu? se matattu kuma tun ayyukan dasukayi wa kasa duk tsawon wannan shekarun, har yanzu ana amfana dasu, irinsu Jami'ar Ahmadu Bello da sauransu, ina shugabannin mu wanda su Sardauna suka rena? Ina Yan k'asa na kwarai? shin kuna tsammanin a bayan ranku za'a tuna daku? Yakamata ku sake tunani kusan irin abinda zaku aikatawa Al'ummarku tun kafin Ajali yazo maku ayimaku Addu'a ba'a la'aceku ba, Sarakuna ku dauki tafarki da Sardauna yabi domin Martabar ku ta dawo a Idanun jama'a, ba wai kutaru a gidan Sardauna, ba kuyi jawabai shike nan, a watse A'a kuyi abinda ze daukaka Al'ummar mu, dare beyiba ga duk wanda yake darai kowa yayi da kyau zega da kyau Allah ya jikansu Ahmadu Bello Amin.

Monday, December 31, 2007

HANA MATA LULLUBA HIJABI A FARANSA

BAYAN HANA MATA LULLUBA HIJABI A FARANSA MATA MUSULMAI SUNKI SU SALLAMA

An zartar da dokan da take hana mata musulmi lullub’a Hijabi, a makarantun kasar Faransa. Sedai Y’an mata musumai sunk’I yarda da hakan, inda suka kasu zuwa gida uku (3)na farko: sune dole tasa suke cire Hijabin a makaranta amma idan sun fita daga makarantan se su lullab’a. Na biyu sune: sun cigaba Luluba Hijabin, hakan yasa suka fuskanci matsi, wanda yakaiga korar dalibai musulmai Mata kimanin d’ari takwas da shida (806). Kashi na Uku kuma sune: wadanda suka gwammace dasubar makarantun gwamnati, sukoma makarantu na kudi daza’a basu daman Lulluba Hijabinsu.

Wannan ke nuna mana cewa ashe Y'ancin dan Adam da k'asashen Turai suke ikirari tsabagen k'arya ce kawai tunda gashi ana nuna ma Musulmi wariya da hanasu sanya tufafin da Addininsu ya Umarcesu dashi. Allah ya ganar damu.

Wednesday, November 28, 2007

Tskanin Yar'adua da Buhari

Bismillahir Rahmanir Rahim
Tun daga sanda akayi zabe a cikin watan Aprilu na bana, wanda yakare da rantsarda Umar Musa Yar'adua, a matsayin zababben shugaban Najeriya, ra'ayoyin mutane suka kasu biyu, da masu goyon baya da masu neman a soke wannan zabe wanda daga karshe kuma shi dan takara da yasha kaye kamar yadda akace wato Janar Muhammad Bukhari me ritaya da jam'iyyarsa suka shigar da kara a gaban kotu suna kalubalantar wannan zabe, da yin kira ga kotu da ta rushe wannan zabe, kamar yanda da dama daga cikin kungiyoyi na gida dana waje sukayi. Yanzu dai ga lokaci na tafiya kuma ga bisa dukkan alama, sashin shari'ah yasamu gyaruwa a wannan lokacin ta inda yasami nasaran soke wasu daga cikin zabubbukan da'akayi na wasu gwamnoni, da wasu yan majalisu na jahohi ko na tarayya, wanda wannan abune da za'ayi tamaka . Asashi daya kuma Umaru Musa Yar'adua gyara yake tayi na abubuwan da gwamnatin da tagabata tayi, wanda bana kan ka'ida ba, kama daga sayarda matatar mai wato NNPC da makamantansu, dayin kokarin samar da man petur a kasa, duk da wasu suna ganin abinda yakeyi kamar siyasa ce kawai saboda cewa beci zabe ba, wanda wasu kuma sun dauka cewa zezo ne yazama dan amshin shatan Obasanjo, to amma koma me kenan dai abubuwa dayakeyi na gyara yakamata ayaba masa akansu, dukda dama hakki ne na kowani shugba daya aikatasu, kai fiyema. Sannan kuma Sarakuna da dattawan Arewa, sukayi taro suna babatu da cewa " Janar da Atiku yakamata su janye wannan karatasu" da dalilin cewa ai duk kansu yan Arewa ne kuma musulmai, na'am wannan magana tasu haka take amma sedai abin tambaya shine meyasa su wannan dattawa kamar yadda ake kiransu aikata wannan aiki, kuma maganar da shi Janar yayi ta bani sha'awa cewa, ai ba Yan Arewa kadai suka zabeshi ba Yan Najeriya ne gaba daya, kuma baso ake a tabbatar da adalci ba kuma shari'a ai abinda zatayi kenan, to mezesa baza'a ajiraba aga abindan kotu zata zartar. kuma kalmar da Yar'adua yayi na cewa duk abinda kotu ta zartar shi zeyi biyayya akan haka kuma bedamu ba, hakan yana nuna cewa yanada halin dattijontaka, kuma abinda yakamacemu mu yan najeriya, da Yan Arewa masu kishi daga cikinsu ba wadanda suka kasheta ba, da mutemaka ma gaskiya da kokarin binta, kuma mutuna cewa kakannin mu ba wani abu yasa har yanzu ake ganin girmansu ba face gaskiya da sukayi da riko da Addininsu irinsu SARDAUNA dasu TAFAWA BALEWA, kuma mudunga karanta tarihi na magabatanmu domin ko ba komi ai Tarihi maimaita kansa yakeyi kuma duk matansa da basu san tarihin magabatansu ba to babu tayanda zasuyi su cigaba. Allah muke roko daya bamu shuwagabanni masu tsoron ALLAH, dazasu kawo cigaban kasa da Addininmu Amiiiiiiiin.

Saturday, October 27, 2007